1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Abu mai kyau ne mu yabi Allahnmu,Abu mai daɗi ne, daidai ne kuma, a yabe shi.
2 Ubangiji yana rayar da Urushalima,Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.
3 Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya,Yakan ɗaure raunukansu.
4 Ya ƙididdige yawan taurari,Yakan kira kowanne da sunansa.
5 Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka,Saninsa ya fi gaban aunawa.
6 Yakan ɗaukaka masu tawali'u,Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.