1 Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum,Ka lura da kukana na neman taimako!Ka kasa kunne ga addu'ata,Gama ni ba mayaudari ba ne.
2 Za ka shara'anta shari'ar da za ta gamshe ni,Saboda ka san abin da yake daidai.
3 Ka san zuciyata,Kakan zo gare ni da dare,Ka riga ka jarraba ni sarai,Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba.Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.
4 Zancen aikin sauran mutane,Na yi biyayya ga umarninkaBan bi hanyar rashin hankali ba.
5 Ina tafiya a kan tafarkinka kullum,Ban kuwa kauce ba.
6 Ina addu'a gare ka, ya Allah,Domin kakan amsa mini,Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.