17 Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,Daga kuma dukan masu ƙina,Gama sun fi ƙarfina!
18 Sa'ad da nake shan wahala suka auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
19 Ya fisshe ni daga cikin hatsari,Ya cece ni, don yana jin daɗina.
20 Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne,Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.
21 Na yi biyayya da umarnan Ubangiji,Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.
22 Na kiyaye dukan dokokinsa,Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.
23 Ya sani ba ni da laifi,Domin na kiyaye kaina daga mugunta.