28 Ubangiji yakan ba ni haske,Allah yakan kawar da duhuna.
29 Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana,Da ikon rinjayar kagararsu.
30 Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai,Maganarsa abar dogara ce!Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.
31 Ubangiji shi kaɗai ne Allah,Allah ne kaɗai kāriyamu.
32 Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.
33 Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.
34 Yakan horar da ni don yaƙi,Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.