5 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
6 A shan wahalata na kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.A Haikalinsa ya ji muryata,Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza,Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgizaSaboda Allah ya husata!
8 Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.
9 Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
10 Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.
11 Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.