6 Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa,Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki,Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara.
7 Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara,Waɗansu kuwa ga dawakansu,Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!
8 Za su yi tuntuɓe su fāɗi,Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!
9 Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji,Ubangiji zai amsa mana sa'ad da muka yi kira.