12 Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,Dukansu suna kewaye da ni,Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.
13 Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,Suna ruri, suna ta bina a guje.
14 Ƙarfina ya ƙare,Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.Dukan gaɓoɓina sun guggulle,Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.
15 Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.Ka bar ni matacce cikin ƙura.
16 Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,Suka taso mini kamar garken karnuka,Suka soke hannuwana da ƙafafuna.
17 Ana iya ganin ƙasusuwana duka.Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.
18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,Suka jefa kuri'a a kan babbar rigata.