5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta,Nakan kauce wa mugaye.
6 Ya Ubangiji, na wanke hannuwanaDon in nuna ba ni da laifi,Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7 Na raira waƙar godiya,Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,Inda ɗaukakarka yake zaune.
9 Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10 Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11 Amma ni, ina yin abin da yake daidai,Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!