1 Ubangiji ne haskena da cetona,Ba zan ji tsoron kowa ba.Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari,Ba zan ji tsoro ba.
2 Sa'ad da mugaye suka tasar mini,Suna ƙoƙari su kashe ni,Za su yi tuntuɓe su fāɗi.
3 Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,Ba zan ji tsoro ba.Ko da magabtana sun tasar mini,Zan dogara ga Allah.
4 Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,Abu ɗaya kaɗai nake bukata,Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,In yi ta al'ajabin alherinsaDukan kwanakin raina,In roƙi biyarwarsa a can.
5 A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa,Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa,Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.