3 Kada ka kāshe ni tare da mugaye,Tare da masu aikata mugunta,Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.
4 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,Ka ba su abin da ya cancance su!
5 Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,Ko kuma abin da ya halitta,Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.
6 A yabi Ubangiji,Gama ya ji kukana na neman taimako!
7 Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni.Na dogara gare shi.Ya taimake ni, don haka ina murna,Ina raira masa waƙoƙin yabo.
8 Ubangiji yana kiyaye jama'arsa,Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.
9 Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji,Ka sa wa waɗanda suke naka albarka!Ka zama makiyayinsu,Ka lura da su har abada.