15 Kana lura da ni kullum,Ka cece ni daga magabtana,Daga waɗanda suke tsananta mini.
16 Ni, bawanka ne,Ka dube ni da alherinka,Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
17 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Kada ka bari a ci nasara a kaina!Ka sa a ci nasara a kan mugaye,Ka sa su yi shiru a lahira.
18 Ka rufe bakin maƙaryatan canDukan masu girmankai da masu fāriya,Waɗanda suke wa adalai maganar raini!
19 Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka!Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma,Yana da banmamaki.Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.
20 Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane,A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al'ajabi,Sa'ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!