4 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina,Kai ne inuwata.
5 Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni.Za ka fanshe ni, ya Ubangiji,Kai Allah mai aminci ne.
6 Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada,Amma ni na dogara gare ka.
7 Zan yi murna da farin ciki,Saboda madawwamiyar ƙaunarka.Ka ga wahalata,Ka kuwa san damuwata.
8 Ba ka bar magabtana su kama ni ba,Ka kiyaye ni.
9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Gama ina shan wahala,Idanuna sun gaji saboda yawan kuka,Na kuwa tafke ƙwarai!
10 Baƙin ciki ya gajerta kwanakina,Kuka kuma ya rage shekaruna.Na raunana saboda yawan wahalata,Har ƙasusuwana suna zozayewa!