2 Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba,Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.
3 Sa'ad da ban hurta zunubaina ba,Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
4 Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji,Ƙarfina duka ya ƙare sarai,Kamar yadda laima yake bushewa,Saboda zafin bazara.
5 Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka,Ban ɓoye laifofina ba.Na ƙudurta in hurta su gare ka,Ka kuwa gafarta dukan laifofina.
6 Saboda haka dukan jama'arka masu biyayya,Za su yi addu'a gare ka, lokacin bukata.Sa'ad da babbar rigyawa ta malalo,Ba za ta kai wurinsu ba.
7 Kai ne maɓoyata,Za ka cece ni daga wahala.Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka,Domin ka kiyaye ni.
8 Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi,Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.