1 Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji,Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!
2 Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.
3 Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,Ka yi gaba da masu fafarata.Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!
4 Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!
5 Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!
6 Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!