16 Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya,Suna hararata da ƙiyayya.
17 Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji?Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu,Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!
18 Sa'an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama'a.Zan yabe ka a gaban babban taro.
19 Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata!Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!
20 Ba su yin maganar zumunci,A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.
21 Sukan zarge ni da kakkausan harshe,Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”
22 Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan.Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji,Kada ka yi nisa!