2 Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.
3 Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,Ka yi gaba da masu fafarata.Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!
4 Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!
5 Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!
6 Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!
7 Suka kafa mini tarko ba dalili,Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.
8 Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su.Tarkunan da suka kafa za su kama su,Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!