9 Sa'an nan zan yi murna saboda Ubangiji,Zan yi murna, gama ya cece ni.
10 Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji,“Ba wani kamarka!Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi,Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”
11 Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina,Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.
12 Sun sāka mini alheri da mugunta,Cike nake da nadama.
13 Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki,Na ƙi cin abinci,Na yi addu'a da kaina a sunkuye,
14 Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a.Ina tafe a takure saboda makoki,Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.
15 Sa'ad da nake shan wahala,Murna suke yi duka,Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya,Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.