3 Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi,Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.
4 Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,Halinsa ba shi da kyau,Ba ya ƙin abin da yake mugu.
5 Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ta kai har sammai,Amincinka ya kai sararin sammai.
6 Adalcinka kafaffe ne,Kamar manyan duwatsu.Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke.Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi.
7 Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji!Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka.
8 Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka,Kakan shayar da su daga koginka na alheri.
9 Kai ne mafarin dukan rai,Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske,