5 Ka miƙa kanka ga Ubangiji,Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.
6 Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske,Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.
7 Ka natsu a gaban Ubangiji,Ka yi haƙuri, ka jira shi,Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya,Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
8 Kada ka yi fushi, kada ka hasala!Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.
9 Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Amma za a kori mugaye.
10 A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,Za ka neme su, amma ba za a same su ba,
11 Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar,Su ji daɗin cikakkiyar salama.