1 Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi,Don kada harshena yă sa ni zunubi,Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”
2 Na yi shiru, ban ce kome ba,Ko a kan abin da suke da kyau!Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,
3 Zuciyata kuwa ta cika da taraddadi,Bisa ga yawan tunanina, haka yawan wahalata zai zama,Dole ne in yi ta tambaya,
4 “Ya Ubangiji, kwana nawa zan yi a duniya?Yaushe zan mutu?Ka koya mini ranar da ajalina zai auko.
5 “Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina!Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne.Hakika duk mutum mai rai,Bai fi shaƙar iska ba.
6 Bai kuma fi inuwa ba!Duk abin da yake yi banza ne,Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!
7 “A kan me zan sa zuciya, ya Ubangiji?A gare ka nake dogara.