3 Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake ciwoYa mayar masa da lafiyarsa.
4 Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji,Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”
5 Magabtana suna mugayen maganganu a kaina,Suna cewa, “Yaushe ne zai mutu a manta da shi?”
6 Masu zuwa su gaishe ni ba da zuciya ɗaya suke zuwa ba,Sukan tattara duk mugun labari a kainaSa'an nan su je su yi ta bazawa ko'ina.
7 Maƙiyana duk suna raɗa da junansu a kaina,Sukan ɗauka na fi kowa mugunta.
8 Suna cewa, “Yana ciwon ajali,Ba zai taɓa tashi daga gadonsa ba.”
9 Har da shaƙiƙin abokina,Wanda na fi amincewa da shi.Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.