18 Ba mu ci amanarka ba,Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.
19 Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.
20 Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,Muka yi addu'a ga gumaka,
21 Hakika ka gane,Domin ka san asirin tunanin mutane.
22 Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.
23 Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!
24 Me ya sa ka ɓuya mana?Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!