1 Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji,Ka kuma ji ajiyar zuciyata.
2 Ya Sarkina, Allahna,Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
3 A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji,Da safe za ka ji muryata,Da hantsi zan yi addu'ata,In kuma jira amsa.
4 Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,Ba ka yarda da mugunta a gabanka.
5 Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,Kana ƙin mugaye.
6 Kakan hallakar da duk maƙaryata,Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.