1 Ka ji addu'ata, ya Allah,Kada ka ƙi jin roƙona!
2 Ka saurare ni, ka amsa mini,Gama damuwata ta gajiyar da ni tiƙis.
3 Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana,Saboda danniyar mugaye.Sukan jawo mini wahala,Suna jin haushina suna ƙina.
4 Azaba ta cika zuciyata,Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.