3 Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana,Saboda danniyar mugaye.Sukan jawo mini wahala,Suna jin haushina suna ƙina.
4 Azaba ta cika zuciyata,Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.
5 Tsoro da rawar jiki sun kama ni,Na cika da razana.
6 Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya,Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!
7 In tafi can nesa,In yi wurin zamana a hamada.
8 Zan hanzarta in nemi mafakaDaga iska mai ƙarfi da hadiri.”
9 Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.