1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,Gama mutane sun tasar mini,Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!
2 Dukan yini maƙiyana suna tasar mini,Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.
3 Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki,A gare ka nake dogara.
4 Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.Me mutum kawai zai yi mini?