8 Ka san irin wahalar da nake sha,Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?
9 A ranar da na yi kira gare ka,Za a komar da abokan gābana baya,Gama na sani Allah yana tare da ni!
10 Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa,Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa.
11 A gare shi nake dogara,Ba zan ji tsoro ba.Me mutum kawai zai yi mini?
12 Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah,Zan miƙa maka hadaya ta godiya.
13 Domin ka cece ni daga mutuwa,Ka hana a ci nasara a kaina.Saboda haka a gaban Allah nake tafiyaA hasken da yake haskaka wa masu rai.