3 Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu,Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya.
4 Cike suke da dafi kamar macizai,Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,
5 Wanda ba ya jin muryar gardi,Ko kuma waƙar gwanin sihiri.
6 Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah,Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji!
7 Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye,Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.
8 Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi,Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce.Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
9 Kafin tukunya ta ji zafin wuta,Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.