1 Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna,Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!
2 Ka cece ni daga waɗannan mugaye,Ka tsirar da ni daga masu kisankan nan!
3 Duba! Suna jira su auka mini,Mugaye suna taruwa gāba da ni,Ba domin wani zunubi ko wani laifin da na yi ba,
4 Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji,Har da suka gaggauta gāba da ni.Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra'ila!Ka tashi ka taimake ni.