2 Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta.Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!
3 Ka sa jama'arka su sha wahala ƙwarai,Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.
4 Ka ta da tuta ga masu tsoronka,Domin su juya su gudu daga abokin gāba.
5 Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.
6 A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,“Da nasara zan raba Shekem,Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
7 Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,Ifraimu ne kwalkwalina,Yahuza kuma sandana ne na sarauta.
8 Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,Edom kuwa kamar akwatin takalmina.Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”