7 Amma Allah zai harbe su da kibansa,Za a yi musu rauni nan da nan.
8 Zai hallaka su saboda maganganunsu,Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.
9 Dukansu za su ji tsoro,Za su faɗi abin da Allah ya aikata,Su yi tunani a kan ayyukansa.
10 Dukan masu adalci za su yi murna,Saboda abin da Ubangiji ya aikata.Za su sami mafaka a gare shi,Dukan mutanen kirki za su yabe shi.