1 Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.
2 Saboda kakan amsa addu'o'i,Dukan mutane za su zo wurinka.
3 Zunubanmu sun kāshe mu,Amma za ka gafarta zunubanmu.
4 Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe suSu zauna a tsattsarkan wurinka!Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!