16 Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah,Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.
17 Na yi kira gare shi neman taimako,A shirye nake in yabe shi da waƙoƙi.
18 Da ban watsar da zunubaina ba,Da Ubangiji bai ji ni ba.
19 Amma hakika Allah ya ji ni,Ya saurari addu'ata.
20 Ina yabon Allah,Domin bai ƙi addu'ata ba,Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.