1 Da ma Allah ya tashi ya warwatsa maƙiyansa!Da ma su waɗanda suke ƙinsa su gudu!
2 Kamar yadda iska take korar hayaƙi,Haka nan zai kore su,Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta,Haka nan mugaye za su hallaka a gaban Allah.
3 Amma adalai za su yi murna,Su kuma yi farin ciki a gaban Allah,Za su yi murna ƙwarai da gaske.
4 Ku raira waƙa ga Allah,Ku raira waƙar yabo ga sunansa,Ku yi hanya ga wanda yake ratsa gizagizai.Sunansa kuwa Ubangiji ne, ku yi murna a gabansa!
5 Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa,Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye,Wato matan da mazansu suka mutu.
6 Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki,Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi,Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.
7 Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah,Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,