11 Ubangiji ya ba da umarni,Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,
12 “Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”
13 Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa,Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)
14 Sa'ad da Allah Mai Iko DukkaYa warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon,Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.
15 Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?
16 Me ya sa, daga manyan kawunankaKake yi wa dutsen da Allah ya zaɓaYa zauna a kai, duban raini?A nan Ubangiji zai zauna har abada!
17 Daga Sinai da dubban manyan karusansa,Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.