19 Ku yabi Ubangiji,Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,Shi ne Allah wanda ya cece mu.
20 Allahnmu, Allah Mai Ceto ne,Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu,Wanda yake cetonmu daga mutuwa.
21 Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa,Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.
22 Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan,Zan komo da su daga zurfin teku,
23 Don ku wanke sawayenku a cikin jinin maƙiyanku,Karnukanku kuwa za su lashe iyakar abin da suke so.”
24 Ya Allah, jama'a duka sun ga irin tafiyarka ta nasara,Irin tafiyar Allah, Sarkina, zuwa tsattsarkan wurinsa.
25 Mawaƙa suna kan gaba, mabusa suna biye,A tsakiya kuwa 'yan mata suna kaɗa bandiri.