6 Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!Kada ka bar ni in jawo abin kunyaGa waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!
7 Sabili da kai ne aka ci mutuncina,Kunya ta rufe ni.
8 Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9 Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a HaikalinkaTana iza ni a ciki kamar wuta,Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10 Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi,Jama'a kuwa suka ci mutuncina.
11 Na sa tufafin makoki,Sai suka maishe ni abin dariya.
12 A tituna suna ta magana a kaina,Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.