1 A gare ka, ya Ubangiji, lafiya lau nake,Faufau kada ka bari a yi nasara da ni!
2 Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni.Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!
3 Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka,Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni,Kai ne mafakata da kāriyata.
4 Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye,Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.
5 Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,Tun ina yaro, nake dogara gare ka.