11 Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,Gama ba wanda zai cece shi!”
12 Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah,Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
13 Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini,A hallaka su!Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni,A wulakanta su sarai!
14 A koyaushe zan sa zuciya gare ka,Zan yi ta yabonka.
15 Zan ba da labarin adalcinka,Zan yi magana a kan cetonka duk yini,Ko da yake ya fi ƙarfin in san shi duka.
16 Zan tafi in yi yabon ikonka, ya Ubangiji Allah,Zan yi shelar adalcinka,Naka, kai kaɗai.
17 Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro,Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.