2 Amma ina gab da fāɗuwa,Ƙafafuna sun kusa zamewa,
3 Saboda na ji kishin masu girmankai,Sa'ad da na ga mugaye suna arziki.
4 Ba su jin zafin ciwo,Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.
5 Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha,Ba su da wahala kamar sauran mutane,
6 Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya,Suka sa hargitsi kuma kamar riga.
7 Zuciyarsu, cike take da mugunta,Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.
8 Sukan yi wa waɗansu ba'a,Suna faɗar mugayen abubuwa,Masu girmankai ne su, suna shawaraA kan yadda za su zalunci waɗansu.