5 Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha,Ba su da wahala kamar sauran mutane,
6 Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya,Suka sa hargitsi kuma kamar riga.
7 Zuciyarsu, cike take da mugunta,Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.
8 Sukan yi wa waɗansu ba'a,Suna faɗar mugayen abubuwa,Masu girmankai ne su, suna shawaraA kan yadda za su zalunci waɗansu.
9 Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama,Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,
10 Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu,Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.
11 Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba,Maɗaukaki ba zai bincika ba!”