1 Don me ka yashe mu haka, ya Allah?Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne?
2 Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni,Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa,Don su zama kabilarka.Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!
3 Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai,Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!
4 Abokan gābanka suka yi sowa ta nasaraA inda akan sadu da kai,Sun ƙwace Haikalin.
5 Suna kama da masu saran itace,Suna saran itatuwa da gaturansu.
6 Da gaturansu da gudumarsu,Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.