3 Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai,Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!
4 Abokan gābanka suka yi sowa ta nasaraA inda akan sadu da kai,Sun ƙwace Haikalin.
5 Suna kama da masu saran itace,Suna saran itatuwa da gaturansu.
6 Da gaturansu da gudumarsu,Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.
7 Sun sa wa Haikalinka wuta,Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada,Sun farfashe shi duk.
8 Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.
9 Ba sauran tsarkakan alamu,Ba sauran annabawan da suka ragu,Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.