8 Daga Sama ka sanar da shari'arka,Duniya ta tsorata, ta yi tsit,
9 Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci,Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.
10 Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo.Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.
11 Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa,Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai.Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,
12 Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai,Ya tsoratar da manyan sarakuna.