2 A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji,Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a,Amma ban sami ta'aziyya ba.
3 Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya.Sa'ad da nake tunani,Nakan ji kamar in fid da zuciya.
4 Ba ya barina in yi barci,Na damu har na kāsa magana.
5 Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.
6 Dare farai ina ta tunani mai zurfi,A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.
7 A kullum ne Ubangiji zai yashe ni?Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba?
8 Ya daina ƙaunata ke nan?Alkawarinsa ba shi da wani amfani?