5 Ya ba da dokoki ga jama'ar Isra'ila,Da umarnai ga zuriyar Yakubu.Ya ba kakanninmu ka'idodi,Don su koya wa 'ya'yansu dokokinsa,
6 Saboda tsara mai zuwa ta koye su,Su kuma su koya wa 'ya'yansu.
7 Ta haka su ma za su dogara ga Allah,Ba za su manta da abin da ya yi ba,Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.
8 Kada su zama kamar kakanninsu,Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya.Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,Ba su kuwa yi masa aminci ba.
9 Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibauSuka gudu a ranar yaƙi.
10 Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,Sun ƙi biyayya da dokokinsa.
11 Sun manta da abin da ya aikata,Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.