1 Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai,Ya Allah Mai Iko Dukka!
2 A can nake so in kasance!Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji.Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.
3 Har ba'u ma sukan yi sheƙa,Tsattsewa suna da sheƙunansu,A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu.Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.
4 Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,Kullum suna raira yabonka!
5 Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka,Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.