3 Har ba'u ma sukan yi sheƙa,Tsattsewa suna da sheƙunansu,A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu.Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.
4 Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,Kullum suna raira yabonka!
5 Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka,Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.
6 Sa'ad da suke ratsa busasshen kwari,Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa,Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna.
7 Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu,Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!
8 Ka ji addu'ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna,Ka ji ni, ya Allah na Yakubu!
9 Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu,Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.