3 Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.
4 Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka daina jin haushinmu!
5 Za ka yi fushi da mu har abada?Ba za ka taɓa hucewa ba?
6 Ka daɗa mana ƙarfi, ka yarda ka sabunta ƙarfinmu,Mu kuwa, jama'arka, za mu yabe ka.
7 Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ka taimake mu da cetonka.
8 Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa,Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama,Idan ba mu koma kan al'amuranmu na wauta ba.
9 Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi,Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.