1 Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
2 Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.
3 Ya birnin Allah, ka kasa kunne,Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.
4 “Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya,Zan sa Masar da Babila a cikinsu,Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha,Su ma na Urushalima ne.”